الأحد، 2 فبراير 2014

Libya Ta Samun Nasarar Dauke Kofin Gasar Kwallon Kafa Ta Zakarun Kasashen Afirka Na Cikin Gida &

http://hausa.irib.ir
Yan wasan kwanlon kafa na kasar Libya sun samu nasarar dauke kofin kwallon kafa na kasashen Afirka, a gasar da aka gudanar a kasar Afirka ta kudu wadda ta shafi ‘yan wasan kwallon kafa na cikin gida.


Libya ta samu wannan nasara ce bayan da fitar da kasar Ghana a bugun da kai sai gola a wasan karshe da aka buga a daren jiya, bayan da kayyadadden lokacin wasan ya kare suna kunnen doki, inda Libya ta saka kwallaye 4 a cikin ragar Ghana, ita kuma ta saka guda day arak.
A wasannin kusa da na karshe Libya ta yi galaba a kan Zimbabwe a bugun daga kai sai gola da ci 4-5, yayin da Ghana ta ci Najeriya ita a bugun daga kai sai gola da ci 4-1, wanda hakan ya kai Najeriya da Zimbabwe zuwa wasan fitar da matsayin na uku da hudu, inda Najeriya ta ci Zimbabwe da kwallo daya a cikin mintuna na 85, inda ta zo matsayi na uku, Zimbabwe kuma matsayi na hudu.

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق